Rahoto: ’Yan Najeriya Miliyan 141 Na Iya Rayuwa Cikin Talauci a 2026 – PwC

Wani sabon rahoto kan tattalin arzikin Nijeriya ya nuna cewa aƙalla ’yan Najeriya miliyan 141 ka iya kasancewa cikin talauci a shekarar 2026, lamarin da ke nuna tsananin ƙalubalen rayuwa ga yawancin al’umma.
Rahoton, wanda cibiyar nazarin tattalin arziki ta PwC ta fitar mai taken “Juya Daidaiton Tattalin Arziki Zuwa Ci Gaba Mai Dorewa”, ya bayyana cewa kusan kashi 62 cikin 100 na ’yan Najeriya na iya rayuwa cikin talauci a shekarar 2026, wadda ke gab da zaɓen 2027.
PwC ta ce duk da sabbin manufofin tattalin arziki da gwamnati ta ɗauka, raunin haɓakar kuɗin shiga na hakika da kuma tsananin tsadar rayuwa na iya ƙara jefa iyalai da dama cikin talauci a cikin shekaru biyu masu zuwa.
A cewar rahoton, “An yi hasashen talauci zai ƙaru zuwa kashi 62 cikin 100 sakamakon ƙarancin haɓakar kuɗin shiga da kuma hauhawar farashin kaya.”
Ko da yake ana sa ran hauhawar farashin kaya zai ragu a hankali, PwC ta lura cewa rayuwar iyalai za ta ci gaba da fuskantar matsin lamba, musamman sakamakon tsadar kayan abinci da matsalar gidaje masu sauƙin kuɗi.
Rahoton ya ƙara da cewa abinci na ɗaukar kusan kashi 70 cikin 100 na kuɗin shigar talakawa, lamarin da ke ƙara tsananta ƙuncin rayuwa, musamman yayin da farashin kayan masarufi ke ci gaba da tashi.


