Siyasa

Jam’iyyar Labour Party (LP) ta bukaci Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya gaggauta sanya hannu kan umarni na musamman (Executive Order) domin aiwatar da ’yancin kananan hukumomi a Najeriya

Jam’iyyar ta ce jinkirin daukar matakin na cin karo da hukuncin Kotun Koli da kuma muradun al’ummar ƙasar.

LP ta bayyana cewa duk da hukuncin Kotun Koli na ranar 11 ga Yulin 2024, wanda ya umurci a rika tura kuɗin kananan hukumomi kai tsaye, gwamnonin jihohi na ci gaba da katsalandan a harkokin kuɗin kananan hukumomi.

Jam’iyyar ta zargi wasu gwamnonin jihohi, ciki har da na Jihar Ogun, da amfani da tsarin da ke raunana kananan hukumomi, tare da hana su cin gajiyar ’yancin kuɗaɗensu.

LP ta kuma bukaci Shugaban Ƙasa da ya umarci Ma’aikatar Kuɗi da Ofishin Akanta-Janar na Tarayya su fara tura kuɗaɗen kananan hukumomi kai tsaye ba tare da ƙarin jinkiri ba, tana mai gargaɗin cewa duk wani jinkiri na nuni da raina hukuncin Kotun Koli.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button