Labarai

NDLEA Ta Kama Ƴan Indiya 22 Da Hodar Ibilis Kilo 31.5 a Jirgin Ruwa

Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Ƙasa (NDLEA) ta kama ƴan ƙasar Indiya 22 bisa zargin safarar hodar ibilis mai nauyin kilo 31.5 a wani jirgin ruwa a ranar 2 ga Janairu.

 

Rahotanni sun nuna cewa jirgin ruwan ya taso ne daga Tsibirin Marshall, inda cikin waɗanda aka kama har da matuƙin jirgin da kuma ma’aikata 21.

 

Ko da yake mai magana da yawun NDLEA bai bayar da ƙarin bayani kan lamarin ba, hukumar ta tabbatar da kama mutanen tare da miƙa su ga hukumomin da abin ya shafa domin ci gaba da bincike.

 

Wannan kamen na zuwa ne a daidai lokacin da kasarnan ke fuskantar matsin lamba daga Majalisar Ɗinkin Duniya kan yawaitar safarar miyagun ƙwayoyi.

 

A wani lamari makamancin haka, NDLEA ta kama ma’aikatan jirgi 20 ƴan ƙasar Philippines da ke ɗauke da hodar ibilis kilo 20 a Legas, tare da tarwatsa ƙungiyoyi biyu da ake zargi da safarar miyagun ƙwayoyi zuwa Biritaniya.

 

Hukumar ta ce wadannan nasarori na daga cikin ƙoƙarinta na ƙarfafa yaƙi da safarar miyagun ƙwayoyi da kare lafiyar al’umma.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button