Gidauniyar Yusuf Kashe Kwabo Ta Yi Wa Yara 220 Kaciya Kyauta A Kano

Gidauniyar Yusuf Kashe Kwabo ta gudanar da aikin kaciya tare da rabon magunguna kyauta ga yara 220, a wani shiri na jin ƙai da aka gudanar a Asibitin Ƙofar Naisa, da ke cikin birnin Kano.
An kaddamar da shirin ne a wani taro da ya samu halartar iyaye da masu ruwa da tsaki, inda aka bayyana cewa wannan ne karo na shida da gidauniyar ke gudanar da irin wannan aikin alheri domin tallafa wa al’umma, musamman marasa galihu.
Da yake jawabi a wajen taron, Shugaban Gidauniyar, Malam Yusuf Umar Kashe Kwabo, ya ce an shirya aikin ne domin neman yardar Allah Maɗaukakin Sarki, ba tare da shigar da siyasa ko wata manufa ta daban ba. Ya jaddada cewa burin gidauniyar shi ne taimakon jama’a da sauƙaƙa musu wasu nauye-nauyen rayuwa.
Malam Yusuf Umar ya kuma bayyana fatan Allah Ya cika mizanin iyayensa da suka riga mu gidan gaskiya da lada mai girma, tare da roƙon Allah Ya ci gaba da ba su ikon gudanar da ayyukan alheri a duk shekara.
A nasu bangaren, wasu daga cikin iyayen yaran 220 da aka yi wa kaciyar tare da basu magunguna kyauta, sun nuna matuƙar godiya ga shugabannin gidauniyar bisa jajircewa da dagewa wajen taimakon al’umma. Sun yi addu’a ga jagoran gidauniyar, tare da roƙon Allah Ya ƙara masa lafiya, tsawon rai da daukaka domin ci gaba da irin wannan aikin jin ƙai.




