Miliyan 100 da aka turawa dan gidan IG Egbetokun bisa kuskure ne kuma ya mayar da su – Hedikwatar ƴansanda

Rundunar ’yandandan Najeriya ta ce an tura Naira miliyan 100 zuwa asusun banki na Victor Egbetokun, ɗan Kayode Egbetokun, Sufeto Janar na ’yansanda mai barin gado bisa kuskure, kuma tun daga nan aka mayar da kuɗin.
Bayanin ya biyo bayan wani rahoto da ya karade intanet inda aka yi zargin cewa an tura kuɗin ne daga asusun kuɗaɗen tsaro (security vote) na Gwamnatin Jihar Anambra zuwa asusun Victor.
Da yake magana a shirin Politics Today na Channels Television a ranar Litinin, kakakin ’yansanda, Benjamin Hundeyin, ya ce an gano ma’amalar nan take kuma aka soke ta.
“Za ku tuna lokacin da shi (Omoyele Sowore) ya ce an biya Naira miliyan 100 zuwa asusun ɗan IGP. Nan take na kira ɗan IGP domin jin abin da ke faruwa, sai ya yi min bayani,” in ji Hundeyin.
“Ya ce ya ga Naira miliyan 100 a asusunsa, kuma ya umarci jami’in kula da asusunsa da ya mayar da kuɗin nan take, abin da aka yi.
“Ya fitar da takardar bayanin asusunsa ya nuna min. An tilasta wa matashin ya rufe asusun. Haka kuma ya rubuta takarda zuwa EFCC domin a binciki zargin.”
Hundeyin ya bayyana lamarin a matsayin kuskuren ma’amala, yana mai cewa an mayar da kuɗin zuwa asusun Gwamnatin Jihar Anambra jim kaɗan bayan an samu sanarwar shigar kuɗin.



