Gwamna Abba Ya Raba Motoci 10 da Babura 50 Ga JTF Don Ƙarfafa Tsaro a Kano

Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya ƙarfafa aikin tsaro a jihar ta hanyar bai wa Rundunar Hadin Gwiwa (JTF) motoci 10 da babura 50 domin inganta zirga-zirga, saurin ɗaukar mataki da kuma ingancin ayyukan jami’an tsaro—musamman a kananan hukumomi masu fama da kalubalen tsaro irin su Kiru, Tsanyawa, Kunchi, Ghari, Shanono, Tudun Wada da Doguwa.
Wannan tallafi ya fito ne daga ofishin Daraktan Sabis na Musamman, Umar Baba Zubairu, wanda ya wakilci Darakta Janar na Sabis na Musamman, Manjo Janar Sani Muhammad (rtd).
Kwamandan JTF, AM Tukur, ya samu wakilci ta hannun Chief of Staff ɗinsa.
Taron ya samu halartar wakilan Kwamishinan ’Yan Sanda, DSS, NSCDC, da shugabannin kananan hukumomin Kiru, Tsanyawa, da Gwarzo.
Gwamna Abba ya jaddada cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da bai wa tsaro muhimmanci tare da goyon bayan duk wani haɗin gwiwa da zai kare rayuka da dukiyoyin al’umma a fadin jihar.



