Matsayar Hukumar karota dangane da zargin satar kudin wani lauya’a kano

Hukumar ta KAROTA ta bayyana cewa A.S. Bawa ya karya dokar zirga-zirgar hanya ta hanyar ajiye motarsa a wurin da ba a amince ba.
Jami’an hukumar sun yi ƙoƙarin gano mai motar, amma babu wanda ya san shi a wajen, lamarin da ya sa aka garzaya da motar zuwa hedikwatar KAROTA da ke Club Road, Bompai.
Bayan ya gano motarsa Bawa ya garzaya ofishin KAROTA inda ya fara zagi da cin mutunci ga jami’an hukumar. A cewar hukumar, ya rika faɗin kalamai irin su:
“Kun san ni kuwa? Zan jefa ku cikin tashin hankali, daga ƙasa har sama da shugabanninku!”
Daga baya sai ya bar ofishin cikin fushi, amma ya aika wakilai biyu tare da wasu mutane biyu don su tabbatar da halin da motarsa take ciki. An bude motar a gaban jami’an ‘yan sanda, kuma kafin hakan sai da wakilan nasa suka kira shi a waya suna tambayarsa inda kudin da yake cewa ya bace yake.
A cewar KAROTA, Bawa ya fara cewa kudin da suka bace sun kai ₦350,000, daga baya ya canza ya ce ₦500,000, sannan daga baya ya ƙara ya ce sun kai har ₦950,000 kamar yadda ya rubuta a cikin korafinsa ga Kwamishinan ‘Yan Sanda.
Hukumar ta bayyana mamakinta kan yadda wanda ya kira kansa lauya zai rika yin irin wannan magana mara tushe da nufin bata sunan jami’an KAROTA. Ta ce ba wani abu da aka taba daga cikin motarsa, kuma zargin bacewar kudi abu ne mara hujja.
“Abin mamaki ne yadda mutum da yake cewa lauya ne zai sauka ƙasa har ya rika zagin ma’aikatan gwamnati da kuma kawo zargi mara tushe. KAROTA ba ta da hannu cikin bacewar duk wani kudi a cikin wannan mota,”




