Majalisar Dattawa Za Ta Tantance Farfesa Joash Ojo Amupitan Don Shugabancin INEC

Majalisar Dattawan Najeriya na shirin tantance Farfesa Joash Ojo Amupitan a yau, domin amincewa da nadinsa a matsayin sabon Shugaban Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC).
Wannan mataki ya biyo bayan wasiƙar buƙata da Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya aike wa majalisar domin tantancewar Farfesa Amupitan.
A makon da ya gabata ne Majalisar Ministoci (Federal Executive Council) ta amince da naɗin Farfesa Amupitan, wanda zai maye gurbin tsohon shugaban hukumar INEC, Farfesa Mahmood Yakubu, wanda wa’adinsa ya ƙare.
Bayan tantancewa da amincewar Majalisar Dattawa, ana sa ran Shugaba Tinubu zai rantsar da Farfesa Amupitan domin ya fara gudanar da ayyukansa a matsayin shugaban sabuwar hukumar zaɓe ta ƙasa.
INEC na da alhakin shirya zaɓuka a faɗin ƙasar, kuma naɗin sabon shugaban na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da shirye-shiryen manyan zaɓukan gwamnati da na ƙananan hukumomi a wasu




