Gwamnatin Legas ta haɗa kai da mazauna Lekki kan atisayen tsaro daga iftila’in gobara da Kuma dasa bishiyu

Ma’aikatar Muhalli ta Jihar Legas ta haɗa kai da Ƙungiyar Mazauna da Masu Ruwa da Tsaki na Gidajen Lekki (LERSA) don shirya horo kan tsaro daga gobara da kuma dasa itatuwa.
An gudanar da taron a Sangotedo, inda aka nuna yadda ake amfani da na’urar kashe gobara kai tsaye tare da bayar da shawarwari masu amfani kan yadda za a amsa gaggawa idan gobara ta tashi.
An dasa bishiyoyi goma don haɓaka dorewar muhalli tare da nuna mahimmancin kiyaye yanayi a tsakanin al’ummomin birane.
Dokta Lasisi Adedoyin, mataimakin darakta a ma’aikatar, ya jaddada muhimmancin gudanar da tantance hadarin gobara a gidaje da ofisoshi.
Ya bayyana nau’ikan na’urorin kashe wuta daban-daban kuma ya lura cewa wasu sun dace da amfani da yawa a cikin gidaje.
Adedoyin kuma ya ba da shawara ga mazauna su yi gyaran wuta sau biyu a shekara kuma su sayi kayan kashe gobara daga dillalai da aka amince da su kawai.
Ya yi kira ga mazauna yankin su Kula da tsaron wuta kamar yadda suke maida hankali wajen tsaro kuma su tanadi kayan kashe gobara a kowane gida.




