
Nafisa, ɗalibar makarantar Nigerian Tulip International College (NTIC), ta doke fiye da mutane 20,000 daga ƙasashe 69, ciki har da ƙasashen da ke amfani da Turanci a matsayin harshen uwa, lamarin da ya ja hankalin duniya ga ilimin Nijeriya.
Gwamna Buni ya bayyana nasarar Nafisa a matsayin wata babbar girmamawa ga jihar Yobe da Nijeriya baki ɗaya, yana mai cewa wannan nasara sakamako ne na zuba jari da gwamnatin sa ke yi a fannin ilimi.
A cewar sanarwar da Mamman Mohammed, Daraktan yaɗa labarai na Gwamnan ya fitar, Nafisa na daga cikin ɗaliban da ke amfana da tallafin karatu daga gwamnatin jihar Yobe, wadda ta riga ta tallafa wa sama da ɗalibai 40,000 a matakin jami’a da sauran manyan makarantu a cikin gida da waje.




