Gwamnatin tarayya ta yi gargadin cewa jihohi 30 da ke kasar nan ciki har da Babban Birnin Tarayya Abuja, suna cikin hadarin ambaliyar ruwa, sakamakon ambaliyar ruwa da ta faru a ranar Alhamis da ta gabata, inda fiye da mutum 200 suka rasa rayukansu a Mokwa na Jihar Neja.
FG/MOKWA

Sannan gidajen da dama sun salwanta, wanda ya sa dubban mutane sun rasa muhallinsu, haka kuma mutum 500 sun bace.
Jihohin da ke fuskantar hadarin ambaliyar ruwa sun hada da Abiya, Adamawa, Akwa Ibom, Anambra, Bauchi, Bayelsa, Benuwai, Borno, Krus Ribas, Delta, Ebonyi, da Edo.
Sauran sun hada da Gombe, Imo, Jigawa, Kebbi, Kogi, Kwara, Legas, Nasarawa, Neja, Ogun, Ondo, Osun, Oyo, Ribas, Sakkwato, Taraba, Yobe, Zamfara da Babban Birnin Tarayya Abuja.
Ministan Albarkatun Ruwa da Tsabtace Muhalli, Injiniya Joseph Utseb, wanda ya bayyana damuwar a wani taron a Abuja, ya kuma ce ambaliyan ruwa a Mokwa ba ta hanyar sakin ruwa daga dam din Kainji da Jebba ba ne, amma sakamakon ruwan sama mai yawa, wanda ya karu sakamakon tasirin canjin yanayi ya haifar da shi.