
Dilolin ƙwayar da aka kama sun haɗa da mata 11 da maza 18, lamarin da ya haifar da fargaba gane da yaɗuwar ɗabi’ar ta’ammali da miyagun ƙwayoyi a tsakanin iyalan sojoji da fararen hula da ke makwabtaka da su.
Kakakin Cibiyar Horas da Mayaƙan Ƙasa da ke barikin, Kyaftin Olusegun Abioye, ya bayyana cewa sojoji sun gano cibiyar dilolin ƙwayar ne a unguwanni Railway da Unguwar Lauya da ke cikin harabar barikin na Jaji.
Ya ƙara da cewa an kama shugabannin masu fataucin miyagun ƙwayoyi guda aƙalla 15 a waɗannan unguwanni biyu, kuma an miƙa duk waɗanda aka kama ga Hukumar Yaƙi da Ta’ammali da Miyagun Ƙwayoyi ta Ƙasa (NDLEA).


