Labarai
Shirin Abinci na Majalisar Ɗinkin Duniya (WFP) ya bayyana cewa daga ƙarshen watan Yuli, zai dakatar da tallafin gaggawa na abinci da kiwon lafiya ga mutane miliyan 1.3 a arewa maso gabashin Najeriya saboda ƙarancin kuɗi.

Wannan na faruwa ne a daidai lokacin da tashe-tashen hankula ke ƙaruwa, kuma yunwa ya kai matsayi mafi muni a tarihin ƙasar.
WFP ya ce kayan abinci da na kiwon lafiya sun ƙare gaba ɗaya, kuma rabon da ake yi yanzu shi ne na ƙarshe.
Idan ba a samu tallafi cikin gaggawa ba, mutane da dama za su fuskanci yunwa, gudun hijira ko kuma shiga hannun ‘yan tada ƙayar baya.
Daraktan WFP a Najeriya, David Stevenson, ya ce kusan mutane miliyan 31 ke fama da matsanancin yunwa a ƙasar wanda shine mafi yawa a tarihi.
Shirin na buƙatar dala miliyan 130 domin cigaba da ayyukanta har zuwa ƙarshen shekarar 2025.




