Labarai

Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu, ya kaddamar da sabon aikin noma na zamani da zummar kara samar da wadataccen abinci a Nijeriya.

Har ila yau, shirin ya kunshi rabar da kayan aikin noma na zamani daidai har guda 9,022, wadanda suka hada da Taraktocin noma,kayan yin girbin amfanin gona da kuma sauran wasu kayan aikin noma.

Tinubu ya ci gaba da cewa, gwamnatinsa ta dauki fannin aikin noma da matukar muhimmanci, domin fannni ne da ke samar da wadataccen abinci ga ‘yan kasa.

Haka zalika, shugaban ya kuma sanar da wadanda suka halaccin taron kaddamar da shirin tabbacin cewa; wadannan ayyuka na noman zamani, za su kara taimakawa wajen kara samar da ayyuka a fannin aikin noma sama da 2,000.

Ya ci gaba da cewa, kayan za su kuma taimaka wajen kara ayyukan masana’antun kasar da samar da damar gudanar da yin bita da kuma kwararrun kayan aikin noma 9,000.

Shugaban ya jaddada muhimmancin yin amfani da kayan aikin noma na zamani, wanda hakan zai taimaka wa manoman wannan kasa

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button