Labarai

Yabon gwani ya zama dole, gomnan jahar Kano Eng. Abba Kabir Yusuf ya dauki nauyin yi wa marassa lafiya aiki kyauta a dukkan qananan hukumomin jihar guda 44.

Hon. Badamasi Mustafa kansilan lafiya na qaramar hukumar Tudunwada jahar Kano, shine ya shaida ma Ahrasjo news cewa: Gomnan jihar Kano ya ɗauki nauyin yi wa mutane masu larurori aiki kyauta a dukkan faɗin qananan hukumomin guda 44.

Wanda cututtukan da ake yin aikin nasu sun haɗar da mata masu larurar fitar gaba, ciwon qaba, ciwon malolo, matsalar haniya, da dai sauran matsalolin da suke addabar al’umma, duba da yanayin da al’umma take ciki, wasu talakawan suna rasa rayukansu saboda larurar ta girmama kuma basu da kudin da za’a yi musu aiki.

Ya ce, wannan shine dalilin da yasa gomnan jihar Kano ya rufe idanu, sannan ya daki qirji ya zage damtse domin ganin ya sharewa talakawan shi hawaye ya raba su da wadannan cututtukan da suke addabar su.

Hon. Badamasi Mustafa ya qara da cewa dama shi gomnan jahar Kano bashi da wani buri face ya ga al’ummar shi ta sami salama, ta zauna lafiya hankalin ta a kwance, wannan shine zai sa shima ya iya samun nutsuwa saboda sanin hakkin ɗan-adam.

Yana mai cewa shi gomnan jihar Kano ba ya bada aiki kuma ya zauna yana barci, tsarin gomnan jihar Kano shine yana duba mai kamar zuwa sannan ya aike shi, kuma bayan ya aika zai shirya tsaf domin yin rakiya har sai ya tabbatar da cewa sakon ya isa inda ya kamata ya isa.

Hon. Badamasi Mustafa yace wannan shine dalilin da ya sanya a qaramar hukumar Tudunwada aka dora mini alhakin kula da wannan aiki a qaramar hukumar Tudunwadar, don haka ko yawo bana zuwa, ina nan na yi tsayin-daka har sai na tabbatar an kammala wannan aiki bisa tsari da qa’idojin da aka bani umarni.

A inda yake qara tabbatar mana kuma ya nuna ma wakilin Ahrasjo news Mutanen da a yau Juma’a aka yi wa aiki kyauta har kimanin zunzurutun mutane tamanin da ukku (83) duk ƴan qaramar hukumar Tudunwada.

Shaidun gani da ido sun tabbatar wa da wakilin Ahrasjo news cewa an yi wa mutanen 83 aiki kyauta, kuma babu wanda aka sami matsalar aikin shi.

Hon. Badamasi Mustafa ya qara jaddada mana cewa, qwararrun likitoci ne suke yin wannan aikin domin ganin rayuwar talakawa ba’a dora ta saman faranti tana walagigi ba.

Sannan Hon. Badamasi Mustafa ya ce muna yi ma Allah S.W.A godiya domin an yi aiki lafiya cikin nasara, babu aikin da aka sami matsala ko kadan a yayin gudanar da shi, ya ce su kansu likitocin muna rokon Allah ya saka musu da alkhairi, domin sun yi aiki da qwarewa cikin nutsuwa tare da girmamawa da mutunta marassa lafiya, wanda haka ake son a sami likitoci suna gudanar da ayyukan su.

Hon. Badamasi Mustafa yace gobe Asabar aikin zai ci gaba Insha Allahu, kuma zan ci gaba da tsayuwa ina sanya ido domin tabbatar da an kammala wannan aiki a qaramar hukuma ta lafiya.

Ya qara da cewa mu ƴaƴan Kwankwasiyya, amana itace taken mu, babban jagoran mu wato Eng. Rabi’u Musa Kwankwaso shine ya horas da mu riko da amana, don haka ba za mu taba saɓa amana ba, kuma mun yi alqawarin yin aiki tuquru domin baiwa maraɗɗa kunya.

Hon. Badamasi Mustafa ya ce babu wata amana da zai karba daga shugabar qaramar hukuma ko daga gomnan jihar Kano face ya isar da wannan amanar kamar yadda aka bashi umarni, domin cika alqawari da isar da amana tarbiyya ce wadda na samu tun a gaban iyaye na.

A inda ya rufe bayanan shi da cewa muna rokon Allah da ya taimaka wa babban jagora wato Eng. Rabi’u Musa Kwankwaso, sannan Allah ya yi riqo da hannun gomnan jihar Kano Eng. Abba Kabir Yusuf ya taimaka masa, domin Allah shine gatan shi kuma shine madogarar shi.

Ya qara da yi ma qaramar hukumar Tudunwada da shugabancin qaramar hukumar addu’ar samun nasarori akan dukkan ayyukan da suka sanya a gaba, tare da fatan Allah ya qara yi ma Tudunwadar albarka, da jihar Kano dama qasar Nigeria baki daya.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button