Gwamnatin jihar Kano ta ƙaddamar da kalandar Musulunci na shigowar sabuwar shekarar Musulunci a yayin taron murnar shiga sabuwar shekara da aka gudanar a rufaffen ɗakin wasanni na Sani Abacha da ke Ƙofar Mata.

Taron ya sami halartar malaman addini da ɗalibai daga makarantun Islamiyya daban-daban Na jihar Kano.
Yayin taron Mataimakinsa gwamnan Kano Kwamared Aminu Abdussalam ya ce wannan taro da ake ran 1 ga watan Muharram hijirar Ma’aikin Allah na shekara 1447, suna yi wa Allah godiya da ganin ranar da aka rufe shafin shekara 1446 wacce ta ƙare.
Mataimakin Gwamnan ya ce Gwamnan jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf ya ce a yi wa kowa barka da sabuwar shekara, kuma yana yi wa al’ummar jihar Kano fatan alheri a cikin wannan shekara da ta shigo da yi musu albishir na ƙara ƙoƙari wajen ƙara sama wa al’ummar jihar sauƙi da samar da kayayyaki na ingantuwar rayuwa.
Ya kara da cewa rana ce ta sabunta niyya na cigaba da fafutukar inganta ilimin addini da na zamani da inganta harkokin tsaron rayuka da dukiyar al’umma tare da yaƙi da shanye-shayen ƙwayoyi da barna da taɓarɓarewar tarbiyya ta matasa a wannan jihar.




