Ketare
Shugaban kasar Ivory Coast, Alassane Ouattara wanda ke jagorantar ƙasar tun daga shekarar 2011, na fuskantar suka na neman mayar da shugabancin ƙasar mutu ka raba.

Wannan dai na zuwa ne bayan Ouattara mai shekaru 83 ya tabbatar da aniyar sake takara wa’adi na hudu a zaben da za a yi ranar 25 ga watan Oktoba.
A wani takaitaccen bayani da ya yi, Ouattara ya ce takararsa ta samo asali ne daga buƙatarsa ta kiyaye zaman lafiyar ƙasa a daidai lokacin da ta ke fuskantar kalubalen tsaro da na tattalin arziki.
Sanarwar da ya yi a kafafen sada zumunta, na zuwa ne bayan da jam’iyyarsa ta RHDP ta amince da takararsa a hukumance.
Jam’iyyun adawa sun soki matakin da cewa ya saba wa kundin tsarin mulkin kasar.
Tun dai gabanin sanar da matsayar sake takara, aka soma tafka muhawara kan soke sunayen ’yan takarar shugaban kasa daga bagaren ’yan adawa.



