Labarai

Iyalan Kanawa da aka kashe a Uromi sun zargin gwamnati da yin watsi da su.

Sun bayyana cewa alƙawarin kuɗin asibiti da tallafi da kuma diyya fa gwamnatocin jihohin Edo da Kano suka yi musu bai wuce fatar baki ba.

Idan zaa iya tunawa ayarin farautan sun baro garin Fatakwal na Nijar Ribas ne, a hanyarsu ta komawa gida domin bikin Ƙaramar Sallah, amma wasu ’yan banga a Uromi suka tare su, suka yi musu kisan gilla.

Akasarin mafarautan sun fito ne daga yankin Toronkawa da ke Ƙaramar Hukumar Bunkure ta Jihar Kano, tare da abokansu daga ƙananan hukumomin Garko da Kibiya da Rano.

‘Yan kaɗan daga cikinsu ne suka sha da ƙyar a harin na Uromi na ranar 28 ga watan Maris, wanda ya sha tofin Allah-tsine daga ɓangarori daban-daban.

’Yan sanda sun bayyana cewa sun kama mutum 14 bisa zargin hannunsu a harin, a yayin da gwamnatocin jihohin Kano da kuma inda abin ya faru, suka yi alƙawarin ɗaukar matakan da suka dace na tallafi ga waɗanda abin ya shafa da iyalansu da kuma tabbatar da cewa an hukunta masu laifin.

Amma sun ce har yanzu shiru suke ji daga dukkanin bangarorin.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button