Labarai
Ma’aikatan jinya karkashin inuwar kungiyar ma’aikatan jinya dana ungozoma dake aiki a cibiyoyin lafiya na gwamnatin taraya sun kara jadada cewar yajin aikin gargadi na kwanaki bakwai da suka yi niyyar tafiya zai fara a yau Laraba.

Mambobin kungiyar sun sha alwashin tafiya yajin aikin ko da kuwa gwamnatin taraya ta kira su domin zama a teburin sulhu.
Da yake bayani ga manema labarai a ranar talata Shugaban kungiyar na kasa Morakinyo Rilwan yace sun baiwa gwamnatin taraya wa’adin kwanaki 15 domin biya musu bukatunsu amma suka ki yin komai a kai.
Idan za’a iya tunawa a ranar 14 ga watan Yulin wannan shekarar ne kungiyar ta baiwa gwamnatin taraya wa’adin kwanaki 15 domin su biya mata bukatunta domin gujewa tundunarsu yajin aiki amma hakan bai haifar da da mai ido ba.
Rilwan yace idan har bayan yajin aikin gargadin na kwanaki bakwai ya kamala ba tare da wani cigaba ba to zasu sake bayar da wa’adin kwanaki 21 ga gwamnatin kafin su tsnduma yajin aikin sai baba ta gani kuma.




