Ketare

Amurka ta nemi Faransa ta yi magana da Iran kafin tsagaita wuta da Isra’ila

Faransa ta isar da sharuɗɗan tsagaita wuta da Amurka ta gabatar wa Iran tare da Isra’ila bisa roƙon Washington a cikin awanni kafin tsagaita wutar, wata majiya ta diflomasiyyar Faransa ta ce a ranar Laraba.

Sakataren Harkokin Wajen Amurka Marco Rubio ya kira takwaransa na Faransa Jean-Noël Barrot don “shaida masa burin Amurka na tsagaita wuta muddin ba a samu ramuwar gayya daga Iran ba,” a cewar majiyar da aka ambata a kamfanin dillancin labarai na Faransa AFP, a ranar Litinin da daddare.

A farkon wannan makon, Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya yi gargadi cewa halin da ake ciki game da rikicin Isra’ila da Iran ya kasance “maras tabbas”, yana karfafa ra’ayin cewa diflomasiyya ya kamata ta rinjayi karfin soja wajen warware rikicin Gabas ta Tsakiya.

Firaministan Qatar, Mohammed bin Abdulrahman Al Thani, yace ya shawo kan Iran da ta amince da tsagaita wuta da Amurka ta gabatar tare da Isra’ila bayan makaman Iran sun nufi wata sansanin Amurka kusa da Doha, in ji wata majiya da ke da masaniya kan tattaunawar.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button