Labarai

Hukumar lafiya ta duniya WHO ta amince da wata allura da ake yi sau biyu a shekara mai suna Lenacapavir da ke kariya daga kamuwa da HIV.

Wannan muhimmiyar sanarwa na zuwa ne bayan ma’aikatar kula da lafiya ta Amurka ta amince da maganin a watan da ya gabata.

Maganin wanda ake amfani da shi ta hanyar yin allura, zai maye gurbin maganin da ake sha kullun ko kuma wasu magungunan da ke aiki na gajeren lokaci.

Shugaban Hukumar Tedros Adhanom Ghebreyesus ya ce amincewa da maganin shi ne matakin farko na faɗaɗa samar da shi.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button