Labarai
NUJ Online Media Chapel Ta Yi Jimamin Rasuwar ‘Yan Majalisar Kano Biyu

A wata sanarwa ta ta’aziyya, ƙungiyar ta bayyana rasuwar ‘yan majalisar a matsayin babban rashi ga Jihar Kano, tana mai cewa sun bar giɓi mai wahalar cikawa sakamakon kwarewa da jajircewarsu wajen hidimar al’umma.
Shugaban ƙungiyar, Kwamared Abubakar Abdulƙadir Ɗangambo, ya miƙa ta’aziyya ga iyalan mamatan, Gwamnan Jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf, Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Kano Rt. Hon. Jibrin Ismail Falgore, da dukkan ‘yan majalisar jihar.
Ƙungiyar ta kuma roƙi Allah Maɗaukakin Sarki da Ya gafarta wa mamatan, Ya kuma bai wa iyalansu da al’ummar Kano juriyar wannan babban rashi.
Hon. Aminu Sa’ad Ungogo da Hon. Sarki Aliyu Daneji sun rasu ne a yammacin ranar Laraba bayan fama da rashin lafiya.




