Labarai
Tsohon sakataren gwamnatin taraya Babachir David Lawan ya bayana cewar al’ummar Arewacin Najeriya na shirin kayar da Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu a zaɓen 2027.

Yace hakan ya faru ne sakamakon ƙuncin rayuwa da kuma tsare-tsaren gwamnatinsa na mayar da yankin saniyar ware.
Ya Kara da cewa gamayyar shugabanni da ’yan siyasar Arewa na haɗa ƙarfi da ƙarfe domin tsayar Da ɗan takara da nufin yaƙar gwamnatin Tinubu a zaɓen 2027.
Babachir David Lawal ya bayya cewa shugabannin siyasar Arewa na aiki tare da Kungiyar Kare Muradun Arewa (ACF) da Kungiyar Dattawan Arewa (NEF) domin cin ma wannan manufa, kuma “Babu yadda za a yi mutum ya ci zaɓe ba tare da samun goyon bayan waɗannan ƙungiyoyin ba.”




