Labarai
Rahotanni daga Daily Trust sun nuna cewa indai ba an samu sauyi ba, Ministan Harkokin Jinƙai da Rage Talauci, Farfesa Nentawe Yilwatda daga Jihar Filato, zai bayyana a yau a matsayin sabon shugaban jam’iyyar APC na ƙasa.

Majiyoyi da dama sun bayyana cewa Nentawe shi ne zaɓin da ya fi fice, sai dai wasu kuma sun ce ana tunanin tsohon gwamnan Nasarawa, Sanata Tanko Al-Makura a matsayin madadin.
Duk wanda ya samu nasarar fitowa a yau zai maye gurbin shugaban riko, Ali Bukar Dalori daga Borno, wanda aka ce ba zai ci gaba da shugabancin na rikon shugabancin jam’iyyar ba, saboda dalilai da suka haɗa da kasancewarsa daga jiha ɗaya da Mataimakin Shugaban Ƙasa.
Rahotanni sun ce Tinubu na buƙatar shugaban jam’iyya mai aminci da biyayya kamar yadda Sanata Adamu ya kasance ga Buhari.




