Ketare

Ramaphosa ya yi adawa da harajin kashi 30% da Trump ya kakabawa Afirka ta Kudu

Shugaban Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa ya yi adawa da abin da ya kira “na kashin kai” karin harajin ciniki da Amurka ta kakabawa kasarsa.

Shugaban Amurka Donald Trump ya sanar a ranar Litinin cewa zai sanya sabon harajin kashi 30% kan kayayyakin da ake shigo da su daga Afirka ta Kudu daga 1 ga Agusta.

Shine kawai ƙasar daga Afirka ta kudu da Sahara da Trump ya ambata a cikin sanarwarsa, yana nuna dangantaka mai tsauri da gwamnatin Ramaphosa.

A cikin wata wasika da ya aika wa Ramaphosa, Trump ya ce dangantakar kasuwanci tsakanin Afirka ta Kudu da Amurka “abin takaici ne, ba ta kasance mai daidaito ba”. A cikin martaninsa, Ramaphosa ya jaddada cewa harajin kashi 30% “ba ya wakiltar bayanan kasuwanci da ake da su daidai”.

Shugaban Amurka ya dakatar da duk wani tallafi ga Afirka ta Kudu, yana zarginta da nuna wariya ga ‘yan tsirarun farar fata. Afirka ta Kudu ta sha musanta wannan zargi.

Ramaphosa ya yi tattaunawa da Trump a watan Mayu domin kokarin gyara dangantaka.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button