Ketare

Iran ta yanke ma wasu ƴan leqen asirin Isra’ila mutum uku hukunci kisa.

Kamfanin dillancin labarai na sashen shari’a a Iran ya ruwaito cewa a yau Laraba ne aka zartar da hukuncin kisa kan wasu mutane uku bayan samunsu da laifin haɗa kai da hukumar leƙen asirin Isra’ila Mossad.

Kamfanin Mizan ya ƙara da cewa an kuma samu mutanen uku da laifin yunƙurin safarar kayan aikin da aka yi amfani da su wajen aikata kisan kai.

A cikin yan makonnin da suka gabata Iran ta zartar da hukuncin kisa kan mutane da dama sakamakon kama su da laifuka makamantan wannan.

Rahotanni na cewa ƙasar ta kama ɗaruruwan mutane da ake zargi da alaƙa da Isra’ila yayin rikicin kwana 12 da aka yi tsakanin ƙasashen biyu.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button