Labarai
Kungiyar kare ‘yancin ɗan adam ta yankin Arewa ta Tsakiya (CLO) ta bayana cewar koƙarin hana Sanata Natasha Akpoti-Uduagha daga ci gaba da aiki a Majalisar Dattawa barazana ce ga cigaban dimokuraɗiyya a Nijeriya.

Ko’odinatan kungiyar Kwamared Steve Aluko ne ya bayyana hakan a wata hira da jaridar Leadership a Jos, babban birnin jihar Filato, inda ya ce wannan mataki yana ƙara bayyana gazawar Majalisar Dattawa ta 10 wajen kare tsarin mulki da doka.
Ya ce abin da ke faruwa ba ya wakiltar muradun ƙasa, sai dai na wasu mutane da ke da wata manufa ta siyasa.
Ya zargi ofishin Sufeto Janar na ƴansanda da ƙin yin aiki da korafe-korafen da aka aika musu dangane da batun, inda ya ce hukumar ƴansanda ta gaza kare Sanata Natasha da tabbatar da ta koma bakin aiki lafiya bisa doka.
Aluko ya jaddada cewa, muddin babu wani sabon hukuncin kotu da ke soke wanda aka riga aka bayar, to babu wata hukuma ko mutum da zai hana ta komawa aiki.



