Labarai
A talatar nan za a yi jana’izar tsohon shugaban ƙasa Marigayi Janar Muhammadu Buhari a mahaifar shi da ke Daura a Jihar Katsina.

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu da kansa zai ƙarbi gawar Buhari da Azahar kuma tuni ya kafa kwamitin manyan jami’an gwamnati domin gudanar da tsare-tsaren jana’izar.
Tun a ranar Lahadi da Buhari ya rasu, Tinubu ya tura Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya je ya kula da tsare-tsare da kuma rako gawar daga ƙasar Birtaniya inda Allah Ya yi wa tsohon Shugaban rasuwa, zuwa Najeriya.
Tuni aka tsaurara matakan tsaro a garin Daura, inda manyan baƙi daga sassa daban-daban ke ta tururuwar zuwa domin halartar jana’izar Buhari wanda ya rasu bayan jinya yana da shekara 82 a duniya.


