Labarai

Saro-Wiwa: Mutumin da Tinubu ya karrama bayan shekara 30 da rataye shi

An bayyana shari’ar da aka yi wa Ken Sari-Wiwa a asirce a matsayin ta je-ka na yi-ka kawai

Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya yi wa Ken Saro-Wiwa afuwa, shekara 30 bayan rataye shi, lamarin da ya sha tofin Allah tsine daga sassan duniya.

Tare da sauran mutane takwas masu hankoro, kotu ta samu Mista Saro-Wiwa da laifin kisan kai inda ta yanke masa hukuncin kisa, sannan aka zartar da hukuncin ta hanyar rataye shi a shekarar 1995 karkashin gwamnatin mulkin soja ta wancan lokacin.

Sai dai mutane da dama sun yi zargin cewa an masu wannan hukuncin sanadiyyar zanga-zangar da suka jagoranta ta adawa da ayyukan manyan kamfanonin hakar man fetur a yankinsu na Ogoniland, musamman kamfanin Shell. Shell ya musanta hannu a kisan mutanen.

Duk da cewa an yi maraba da afuwar da Tinubu ya yi wa mutanen, wasu masu hankoro da kuma yan’uwan wadanda aka kashe sun ce hakan bai wadatar ba.

Baya ga yi masu afuwa, shugaban na Najeriya Bola Tinubu ya kuma karrama Saro-Wiwa da sauran masu hankoron tara – wadanda ake wa lakabi da ‘Ogoni nine’ – da lambar girmamawa ta kasa.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button