Jami’ar Columbia ta dakatar, da kusan dalibai 80 saboda zanga-zangar Gaza

Jami’ar Columbia a Amurka ta kakabawa ɗalibai da dama hukunci mai tsanani, ciki har da kora, dakatarwa daga karatu da kuma soke digirin karatu, saboda shiga zanga-zangar nuna adawa da yaƙin Isra’ila a Gaza.
Kungiyar dalibai masu rajin kare hakkin dan Adam ta Jami’ar Columbia, wato Columbia University Apartheid Divest (CUAD), wadda ta yi kira ga makarantar da ta yanke duk wata alaka ta kudi da Isra’ila, ta bayyana a cikin wata sanarwa cewa kusan dalibai 80 yanzu an kora su ko dakatar da su har na tsawon shekaru uku saboda shiga zanga-zangar adawa da yaki.
A ranar Talata, Columbia ta ce a cikin wata sanarwa cewa hukuncin da ta yanke na baya-bayan nan ga ɗalibai yana da alaƙa da “tashin hankali a ɗakin karatu na Butler a watan Mayu 2025 da kuma sansanin yayin Makon Alumni a shekarar 2024”.
Zanga-zangar dalibai masu goyon bayan Falasdinawa a Jami’ar Columbia a shekarar 2024 sun taimaka wajen tayar da wani gagarumin yamutsi kan yaki mara sassauci da Isra’ila ke yi wa Falasdinawa a Zirin Gaza.
A karshe wuraren zanga-zangar sun watse lokacin da Jami’ar Columbia ta ba da damar shigar daruruwan ‘yan sandan birnin New York cikin harabar jami’ar, wanda ya kai ga kama mutane da dama.
Duk da tsauraran matakan da jami’ar ta dauka, daliban masu zanga-zanga sun mamaye Laburaren Butler yayin jarabawar karshe a watan Mayun wannan shekara, suna neman a janye hannun jari daga kamfanonin da ke da alaka da sojojin Isra’ila tare da nuna goyon baya ga Falasdinawa a Gaza.




