Ketare

Aƙalla mutane uku sun mutu sakamakon zaftarewar ƙasa da ruwan sama mai tsanani a arewacin Pakistan

Zaftarewar ƙasa da ta afku sakamakon ruwan sama mai karfi na daminar Bana ta kashe akalla mutane uku a arewacin Pakistan, a cewar jami’an yankin, yayin da ake ci gaba da aikin ceto mutane 15 da suka bace.

Fiye da motoci takwas ne aka kwashe a ranar Litinin lokacin da ruwan sama mai karfi ya haifar da malalar kasa a kan babbar hanya a gundumar Diamer ta Gilgit-Baltistan, in ji Abdul Hameed, jami’in ‘yan sandan gundumar Diamer, yayin tattaunawar sa da kamfanin dillancin labarai na AFP a ranar Talata. “An gano gawarwaki uku kuma fiye da 15 har yanzu ba a gani ba.”

Ambaliyar ruwa ta rushe gine-gine da kuma katsewar wutar lantarki ya haifar da mutuwar mutane 221 tun lokacin da damina ta fara a ƙasar a ƙarshen watan Yuni, tare da ruwan sama mai karfi fiye da yadda aka saba.

 

Wasu daga cikin waɗanda abin ya shafa masu yawon buɗe ido ne daga sassa daban-daban na Pakistan da suka zo ziyartar wurin yawon buɗe ido na Gilgit-Baltistan, wani lardi a Kashmir da Pakistan ke Iko dashi.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button