Ketare
Rundunar sojin Isra’ila ta umarci Falasɗinawa su ƙaurace wa wani yanki na tsakiyar zirin Gaza, inda ba ta ƙaddamar da samame ta ƙasa ba tun bayan fara kai hare-hare a 2023.

Rundunar ta ce mutanen da ke samun mafaka a unguwar Deir al-Balah su fice nan take su koma yankin al-Mawasi da ke kusa da kogin Baharrum.
Umarnin da ke nuna shirin fara kai hare-hare ya jawo fargaba da ruɗani tsakanin dubun dubatar Falasɗianawa da iyalan Isra’ilawan da Hamas ke riƙe da su waɗanda ke tunanin ana riƙe da su ne a wurin.
Sojojin Isra’ila sun kai hare-hare ta sama a yankin amma ba su taba kai samame ta ƙasa ba.




