Ketare
An ceto ma’aikatan haƙar ma’adanai 18 bayan sun shafe awa 18 a cikin ramin mahaƙar gwal da ke arewacin ƙasar Colombia.

Gwamnatin ƙasar ta ce ma’aikatan sun maƙale ne a ranar Alhamis a mahaƙar El Minón sakamakon matsalar kayan aiki, kamar yadda kamfanin labarai na AFP ya ruwaito.
Bayan shafe awa 12 ana aikin ceto, mutanen sun fito cikin ƙoshin lafiya, in ji hukumar kula da haƙar ma’adanai ta Colombia.
Cikin wata wasiƙa da ya aike wa gwamnatin tarayya, magajin garin Remedios ya ce mahaƙar ba ta da lasisi.
Sai a ranar Juma’a da ƙarfe 3:00 na rana agogon ƙasar (9:00 na dare agogon Najeriya) aka kammala aikin zaƙulo su.




