Labarai
Hukumar kula da gyaran hali ta jihar Kano ta bayyana cewa daurarru 58 ne suke rubuta jarabawar kammala sakandare ta NECO.

Hakan na cikin wata sanarwa da kakakin hukumar Musbahu Lawan Kofar Nasarawa ya fitar.
Ya bayyana cewa suna rubuta jarabawar ne dalilin biya musu kudin da gwamnatin jihar Kano tayi.
Sanarwar tace hakan zai taimaki daurarrun musamman a bangaren ilimi dangane da rayuwarsu ta gaba, bayan kammala zama a gidan gyaran halin.



