Labarai
Shugaban majalisar dattawa Sanata Godswill Akpabio, ya kwatanta marigayi shugaban kasa Muhammadu Buhari a matsayin shugaba na gari wanda ya mulki Najeriya ba tare da satar duƙiyar ƙasa ba.

Akpabio, wanda ya bayyana haka a lokacin taron majalisar zartaswa da aka gudanar a Abuja don yi wa tsohon shugaban addu’o’i, ya ce masu sukarsa ma sun san cewa bai yi almubazzaranci da duƙiyar ƙasa ba lokacin da yake mulki.
“Maganar gaskiya ita ce Buhari mutum ne wanda ba a isa a tankwarashi ba. Bai guje wa nauyin da aka ɗora masa ba, mutumin da kuma ya bauta wa ƙasarsa yanda ake so.
“Shugaba ne da ya jajirce wajen yin mulki yanda ya kamata duk da kalubale da ya fuskanta. Hakan bai sa gwiwarsa ta sare ba, amma duk da haka wasu sun ki aminta da shi,” in ji Akpabio.
Taron majalisar zartaswar na musamman ya samu halartar shugabancin majalisar tarayya, ministoci, gwamnoni da kuma ƴaƴan marigayin.




