Labarai

Ma’aikatar Ilimi ta kasa a ranar Juma’a ta ce an sanya wa jami’ar Maiduguri sunan marigayi tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ne sakamakon jajircewar da Buhari ya yi a fannin ilimi.

Daraktan yada labarai na ma’aikatar ilimi Folasade Boriowo ne ya bayyana hakan a wata sanarwa.

A cewar sanarwar, shugaba Bola Tinubu ya amince da sauya sunan ne a wani zama na musamman na majalisar zartaswa ta tarayya da ta kira domin karrama marigayin.

Shugaban ya bayyana Buhari a matsayin dan kasa na gari wanda gwamnatinsa ta fifita tsaron kasa, farfado da tattalin arzikin kasa, gyara hukumomi, da yaki da cin hanci da rashawa.

Ma’aikatar ilimi ta kuma bayyana sauya suna a matsayin wata alama da ke tabbatar da abin da Buhari ya bari.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button