Hare-haren Isra’ila sun kashe akalla 51 yayin da Trump ke nuna ci gaba a tattaunawar Kan rikicin Gaza

Hare-haren Isra’ila sun kashe akalla mutane 51 a Zirin Gaza, ciki har da Falasdinawa 14 da suke jiran taimako a wuraren rarraba kayan agaji, majiyoyin likitoci sun shaida wa Al Jazeera, duk da cewa Shugaban Amurka Donald Trump ya ce ana samun “gagarumin ci gaba” wajen kawo karshen yakin.
Majiyoyi a asibitocin al-Awda da Al-Aqsa Martyrs a Gaza sun shaida wa Al Jazeera cewa akalla Falasdinawa tara ne aka kashe kuma wasu da dama sun jikkata sakamakon harbin Isra’ila a farkon ranar Laraba yayin da suke jiran taimako a kusa da Netzarim Junction a tsakiyar Gaza.
Kisan gilla ya kasance sabon tashin hankali a wuraren rarraba tallafi da aka kafa a ƙarshen watan da ya gabata ta hanyar Gaza Humanitarian Foundation (GHF) da Isra’ila da Amurka ke goyon baya.
Yayinda Isra’ila ke ci gaba da hare-harenta, sojojinta sun ce an kashe sojoji bakwai a fafatawa a Gaza a ranar Talata.




