Wasu ‘yan bindiga sun kai mummunan hari a kauyen Rim da ke Jihar Filato, inda suka kai wa wasu da ke dawowa daga binne gawa farmaki, suka kuma yanke wa ɗaya daga cikin matasan da ke cikin su hannu.

Rahotanni sun bayyana cewa mutanen na kan hanyarsu ta dawowa daga jana’izar wani mamaci a kauyen Bachit, wanda ke makwabtaka da Rim, lokacin da suka ci karo da maharan da suka bude musu wuta ba tare da wani dalili ba.
Daya daga cikin wadanda suka sha da kyar a harin, wanda kuma hadimin Gwamnan Filato Caleb Mutfwang ne, Timothy Dantong, ya tabbatar da aukuwar lamarin a ranar Ya bayyana cewa harin ya auku ne bayan sun bar wajen jana’izar.
A cewar Timothy, “Jiya na halarci jana’iza a kauyena na Bachit. A hanyarmu ta dawowa muka ji an kai hari kauyen Rim. Sai aka ba mu shawarar mu dakata kafin mu ci gaba da tafiya. Mun zauna na tsawon awa biyu muna jira.”
Ya ce wasu daga cikin su sun gaji da jira suka ci gaba da tafiya, amma a cikin tafiyar tasu ne ‘yan bindigar suka bude musu wuta tare da yankewa ɗaya daga cikinsu hannu gaba ɗaya.




