Labarai

Fadar shugaban kasa ta musanta rahoton dake bayyana cewar an zabi sabon sakataren gwamnatin tarayya.

Tace har yanzu George Akume shi ne sakataren gwamnatin sabannin wasu rahotanni da suke yawo a kafafen sada zumunta.

Wannan bayanin na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai baiwa shugaban kasa shawara kan yada labarai Bayo Onanug ya fitar a daren Jiya Asabar.

Sanarwar tace shugaba Tinubu wanda a yanzu haka ke ziyarar aiki a birnin St Lucia bai yi wani sabon nadi ba kafin tafiyarsa.

Rahotanni sun bayana cewar wannan sanarwar dai ta biyo bayan wani labari da yake yawo a shafukan sada zumunta na cewar shugaban ya nada Hadiza Bala Usman a matsayin sabuwar sakatariyar gwamnatin tarayya.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button