Labarai

Kwanaki kadan da gwamnatin jihar kano ta shawarci mutan kano da su kare kansu da harin masu kwacen waya wasu unguwanni sufara daukan mataki

Al’ummar unguwar Tudun wada Bompai dake karamar hukumar Nassarawa, karkashin jagorancin Sarkin Tudun wada Alh Ibrahim Aliyu sun gudanar da wani gangami na babu sani babu sabo, kan yaki da kwacen waya da haura gidajen mutane da shaye-shaye da ake yawan yi a yankin.

An gabatar da gangamin ne da Dattawan mazabar da dagaci da masu unguwanni da kuma shugabancin Tundun wada Foundation Karkashin Comr Ibrahim Abdullahi Usman.

Kazalika an yi gangamin ne tare da matasa da yan sanda da sojoji da DSS da kuma civil Defence da Hisba da kuma sauran Al’ummar yankin.

Yayin gangamin dagacin Tudun wada Alh Ibrahim Aliyu ya ce sun gudanar da taron ne don nuna adawarsu da yadda harkokin tsaro suka tabarbare a unguwar.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button