Labarai
Gwamnatin Tarayya ta ayyana dokar ta-baci kan aikin hanyar Suleja zuwa Minna.

Ministan Ayyuka, David Umahi, ne ya bayyana hakan a jiya Asabar yayin da yake duba aikin hanyar.
Umahi ya ce sake gina hanyar wani aiki ne da gwamnatin Bola Ahmad Tinubu ta gada daga gwamnatin da ta gabata, ya na mai cewa matsalar rashin kammala aikin na da alaka da kamfanonin da aka bawa kwangilar.
Ya kara da cewa duk ƙoƙarin da aka yi sama da shekara daya da rabi domin su dawo su ci gaba da aikin abin ya ci tura.
Umahi ya ci gaba da cewa Gwamnan Jihar Neja, Muhammad Bago ne ya kai koken kai tsaye ga Shugaba Bola Tinubu, wanda ya bayar da umarni ga Ma’aikatar ayyuka da ta shiga cikin lamarin



