Gwamnatin jahar Lagos ta horar da Mata da Maza 255 sana’oin dogaro dakai

Gwamnatin Jihar Legas, ta hannun Ma’aikatar Harkokin Mata da Rage Talauci (WAPA), ta sake jaddada aniyar ta na karfafa mata ta fuskar kudi ta hanyar shirye-shirye daban-daban.
Mrs Bolaji Dada, Kwamishinar Harkokin Mata da Rage Talauci, ta bayyana wannan a wajen bikin rufe Shirin Karfafa Tattalin Arziki na Kwarewar Rayuwa (LEEP) a Agbowa/Ikosi.
Kamfanin Dillancin Labarai ta Najeriya NAN,ya ruwaito cewa, mata da matasa sama da 250 ne aka ba su kayan farawa bayan kammala horon makonni hudu na LEEP na WAPA a yankin.
An koyar dasu dabarun, yin fenti, zane da rini, kwalliya da ɗaura gele, gyaran gashi, girke-girke, dinkin dutse, man shafawa, magungunan kashe kwari, da kuma samar da sauran kayayyakin gida.
Kwamishinan ya yabawa Gwamna Babajide Sanwo-Olu saboda inganta ci gaban da ya shafi kowa, daidaito tsakanin jinsi, da karfafa gwiwar al’ummomi a fadin jihar.



