Ketare

Bayan Ƙorafi Daga Masu Cajin Waya: An Cafke Matashi Kan Damfara A Sabuwar Gandu

Rundunar tsaro mai yaƙi da faɗan daba, ƙwacen waya da kuma ta’ammali da kayan maye, wato Anti Phones Snatching Force a Jihar Kano, ta cafke wani matashi bisa zargin damfarar waya a yankin Sabuwar Gandu da ke Kano.

Kwamandan rundunar, Nura Salisu Sharaɗa, ya bayyana hakan yayin zantawa da manema labarai, inda ya ce kamen ya biyo bayan ƙorafin da rundunar ta samu daga masu sana’ar cajin waya kan yadda aka damfare su.

A cewarsa, binciken da suka gudanar ya nuna cewa da fari matashin ya kai ƙaramar wayarsa caji, wadda kuɗinta bai wuce naira dubu takwas ba

An ba shi kati (Pass) kamar yadda aka saba.

Sai dai bayan wasu awanni, ya dawo da wani kati mai ɗauke da wata lamba ta daban, inda aka ba shi babbar wayar wani kwastoma da ya kai caji.

Ya ce matashin ya tafi da babbar wayar tare da barin tasa a wajen.

Bayan samun ƙorafi, rundunar ta fara bincike har ta gano inda ake zargin ya tsere a unguwar Sabuwar Gandu, inda daga bisani aka cafke shi.

An ce an samu wayar da ta haura naira dubu 130 a hannunsa, sannan an tarar ya goge dukkan bayanan da ke cikin wayar tare da cire layukanta.

Da yake bayyana nadamarsa, matashin ya ce wannan ne karo na farko da ya aikata irin wannan laifi, yana mai cewa ya fahimci kuskurensa, kuma da yardar Allah ba zai sake aikata hakan ba.

Kwamandan rundunar, wanda aka fi sani da Kossap, ya ce da zarar sun kammala tattara bayanai, za su miƙa wanda ake zargin ga hukumomin da suka dace domin ɗaukar mataki na gaba.

Ya kuma yi gargaɗi ga masu irin wannan dabi’a ta damfara da su daina, domin gujewa shiga hannun hukuma da kuma yin dana-sani a gaba.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button