Labarai

Wata Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a birnin Abuja ta amince da gabatar da wani rahoto daga Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) wanda ake zargin yana da alaƙa da jagoran ƙungiyar (IPOB), Nnamdi Kan, kan kisan ‘yan sanda 186 da rushe ofisoshin ‘yan sanda 164 a lokacin zanga-zangar EndSARS.

Mai shari’a James Omotoso ne ya amince da shigar da rahoton a matsayin hujja yayin ci gaba da sauraron shari’ar da ake yi wa Kanu bisa zargin ta’addanci a ranar Alhamis.

Lauyan gwamnati mai gabatar da ƙara, Adegboyega Awomolo (SAN), ne ya gabatar da rahoton ta bakin wani jami’in DSS da aka bayyana da sunan sirri “Mr EEE” saboda dalilai na tsaro, a matsayin shaida na biyar.

Yayin da yake ba da shaida a gaban kotu, Mr EEE ya ce shi da wasu jami’an DSS an tura su zuwa yankin Kudu maso Gabas da wasu sassa na ƙasar nan domin tattara bayanai da rubuta rahotanni game da tashin hankalin da ya biyo bayan zanga-zangar EndSARS.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button