Labarai
Shugaban hukumar tara kuɗaɗen haraji ta Najeriya Zacch Adedeji, ya ce a ranar 1 ga watan Janairun shekarar 2026 ne sabbin dokokin tattara harajin da shugaban ƙasar ya sanyawa hannu a jiya ne za su fara aiki.

Adedeji ya dai bayyana hakan ne a lokacin da yake yi wa manema labarai jawabi a jiya Alhamis, jim kaɗan bayan sanya hannu don sabuwar dokar haraji da shugaba Tinubu ya yi.
Ya ce tazarar watanni shidan da aka samu, zai baiwa gwamnati damar shiryawa da wayar da kan al’umma da kuma daidaita kasafin kuɗin ƙasar.
Adedeji ya jaddada mahimmancin fara amfani da sauye-sauyen a farkon shekara, yana mai cewar hakan zai baiwa masu ruwa da tsaki damar aiwatar da shi yadda ya kamata saɓanin a tsakiyar shekara.
Akan wannan sabbin dokokin haraji, mun tuntubi Dr. Abdurrazak Ibrahim Fagge malami a tsangayar koyar da ilimin tattalin arziki a jami’ar Northwest.




