Labarai

Kungiyar Malaman Makarantun Kimiyya da Fasaha ta ASUP reshen kwalejin kimiya na Nuhu Bamalli dake Zariya ta bayana cewar albashin da mai hidimar kasa ke dauka yanzu a Najeriya yafi na malaman kwalejin yawa.

Kungiyar ta bayana hakan ne a daidai lokacin da take cigaba da gudanar da yajin aiki wanda suke yi sakamakon rashin kyawun yanayi na koyarwa.

Shugaban kungiyar Usman-Shehu Suleiman ne ya bayyana haka a wata hira da kamfanin dillancin labarai na Najeriya a Zariya ranar Alhamis.

NAN ta ruwaito cewa kungiyoyin ma’aikatan na hadin gwiwa sun shiga yajin aikin gargadi na mako guda a ranar 16 ga watan Yuni, wanda ya hana ayyukan ilimi a bangarori biyu na kwalejin.

Yajin aikin dai ya ta’allaka ne kan rashin aiwatar da tsarin albashin ma’aikatan kwalejin fasaha da kwalejojin ilimi na kasa da kuma aiwatar da shekarun ritaya na shekaru 65 ga wadanda ba su koyarwa da dai sauransu.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button