Gwamnatoci sun fara yunƙurin kwashe ‘yan ƙasarsu daga Isra’ila da Iran

Gwamnatoci a duniya na yunkurin kwashe dubunnan ‘yan kasarsu da rikicin ya barke tsakanin Isra’ila da Iran, suna shirya motocin bas da jirage a wasu lokutan suna taimakawa mutanen da ke tsallakawa kan iyakokin kasar da kafa.
Baƙi sun yi gaggawar barin kasashen biyu bayan Isra’ila ta kaddamar da wani gagarumin hari na bam a ranar Juma’ar da ta gabata da ya nufi wuraren nukiliya da na soja na Iran, wanda ya haifar da martani daga Tehran.
Amma tare da rufe sararin samaniyar Isra’ila kuma kasashen biyu suna musayar harbin makamai masu linzami masu nauyi, ana kwashe mutane da dama daga kasashe na uku.
Kasashen Turai sun riga sun mayar da daruruwan ‘yan kasarsu daga Isra’ila.
Jamhuriyar Czech da Slovakia sun ce a ranar Talata sun mayar da mutane 181 gida a cikin jiragen gwamnati.



