Labarai
Gwamnatin tarayya ta bayyana yiwuwar samun kudaden shiga da yawansu ya kai kimanin Naira tiriliyan uku, a aikin tatsar man Rogo a Nijeriya duk shekara.

Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima ne ya sanar da haka, a taron bikin ranar Rogo ta duniya na 2025, wanda aka gudanar a dakin taro na Bankuet da ke fadar shugaban kasa a Abuja.
Ya sanar da cewa, tuni gwamnatin tarayya ta fara ayyukan kirkirar fasahar zamani, domin zamanantar da masana’antar sarrafa Rogo a wannan kasa.
Kazalika, Shettima ya kaddamar da aikin kimiyya, wanda aka samar da shi don rubunyya Irin Rogon da ake shukawa.
A cewarsa, aikin zai kuma rage gibin da ake da shi na yin noman Rogo, domin samun riba tare kuma da samar da ingantaccen Iri.




