Labarai

Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Namadi Sambo, ya musanta jita-jitar ficewa daga jam’iyyar PDP zuwa APC.

A wata sanarwa daga mai ba shi shawara kan harkokin yaɗa labarai, Umar Sani, Sambo ya ce labarin ba gaskiya ba ne, kuma an ƙirƙire shi ne don ruɗar da jama’a.

Ya bayyana cewa hoton da ake yaɗawa wanda ya nuna shi tare da Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, tsohon hoto ne.

Ya ce sun ɗauki hoton ne shekaru da suka wuce lokacin da gwamnan ya kai masa ziyara a Abuja don jajanta masa bisa rasuwar ɗan uwansa, marigayi Sani Sambo.

wata babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta bayar da belin dakatacciyar Sanatar Kogi ta Tsakiya, Natasha Akpoti-Uduaghan, kan Naira miliyan 50.

Kotun dai, wacce ke karkashin jagorancin Mai Shari’a Chizoba Orji, ta kuma yi watsi da bukatar Gwamnatin Tarayya kan wacce ake karar cewa a kulle ta a kurkuku har zuwa lokacin yanke hukunci.

Mai Shari’ar ta ce ba ta ga dalilin da zai sa ta hana wacce ake karar beli ba, inda ta ce akwai gamsassun hujjojin da ke nuna cewa a shirye take ta fuskanci shari’ar.

Sai dai baya ga Naira miliyan 50 din, kotun ta kuma umarci Sanata Natasha ta gabatar da wanda zai tsaya mata, wanda kuma dole ne ya kasance mutum mai kima kuma wanda yake da kadara a Babban Birnin Tarayya Abuja.

Daga nan ne sai kotun ta dage ci gaba da sauraron karar zuwa 23 ga watan Satumban 2025.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button