Labarai
Hukumar Hisbah za ta daura auren matasa biyunnan da suka taɓa bayyana cewa sun yi aure babu sanin iyayen su.

Shugaban hukumar na karamar hukumar birnin Kano Hamidan Tanko Alasaka, ne ya sanar da hakan lokacin da yake zantawa da manema labarai, yana mai cewa an cimma matsaya tsakanin iyayen yaran da Hisbah, akan cewa za’a daura wannan sabon aure a ofishin Hisbah ta karamar hukumar birni.
Akan haka ne hukumar ke neman al’umma su tallafawa masu niyyar yin auren, musamman waɗanda suka yi alkawarin bayar da tallafin tun da farko.
Yace akwai mutanen da suka yi alkawarin bayar da tallafi ga masu shirin zama ango da amarya amma kawo wannan lokaci tallafin bai zo hannun Hisbah ba.
Idan za’a iya tunawa a kwanakin baya ne, matasan suka ɗaurawa kansu aure ba tare da sanin iyayen su ba, saboda tsananin kaunar da suke yiwa juna.




